Libya

An saki Seif al-Islam Ghaddafi a Libya

Seif al-Islam Ghaddafi na Libya
Seif al-Islam Ghaddafi na Libya REUTERS/Stringer/File Photo

An saki Seif al-Islam, dan marigayi tsohon shugaban Libya Mu’ammar Ghaddafi bayan ya shafe fiye da shekaru biyar a hanun ‘yan tawaye. Rahotanni sun ce an sake shi ne a Libya bayan ya shafe shekaru 5 a tsare.

Talla

‘Yan tawaye da ke rike da ikon birnin Zintan a yammacin Libya sun ce, an saki Seif al-Islam ne a karkashin wani shirin afuwa a cikin watan Ramadan da majalisar gwamnatin gabashin kasar ta amince.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook, kungiyar ‘yan tawayen ta ce tuni Saif al-Islam ya fice daga birnin Zintan bayan sakinsa a yammacin ranar Juma’ar da ta gabata a Libya.

Sai dai babu wani tsayayyen tabbaci game da sakin Saif al-Islam da ake ganin zai dada jefa Libya cikin tashin hankali.

Lauyansa a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Karim Khan ya kasa bada tabbaci ko kuma musanta wannan batu.

Tun a cikin watan Nuwamban 2011 ne, ake tsare da Saif al-Islam bayan ’yan kwanaki da kisan da aka yi wa mahaifinsa a wani bore da ya samu goyon bayan kungiyar Tsaro ta NATO.

Tuni dai mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwansa suka tsere zuwa Algeria kafin daga bisani suka isa Oman bayan boren da ya kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi.

‘Yan tawayen Zintan da ke adawa da gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkjin Duniya ta ki mika Saif al-Islam ga hukumomin Libya duk da tarin shari’oin da ke kansa na cin zarafin bil adama a shekara 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.