Libya

Ana tursasawa ‘yan ci-rani biyan kudin fansa a Libya

Daruruwan 'Yan ci-rani ake garkuwa da su a Libya
Daruruwan 'Yan ci-rani ake garkuwa da su a Libya UNICEF

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kungiyoyin masu safarar mutane a kasar Libya, suna amfani da shafukan sada zumunta na intanet wajen yada cin zarafi da azabtar da ‘yan ci-rani da suka yi garkuwa da su.

Talla

Gungun masu safarar bakin hauren zuwa Nahiyar Turai daga Libya na amfani da wannan dama wajen neman kudaden fansa daga iyalan ‘yan gudun hijirar.

Hoton bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna wasu ‘yan ci-rani daga kasashen Somalia da kuma Habasha kimanin 260 cikin wani mawuyacin hali a wani yanki na kasar Libya da ba a iya tantancewa ba.

A cikin bidiyon wasu daga cikin matasan da aka yi garkuwa da su sun bayyana cewa, ana lakada musu dukan kawo wuka, tare da azabtar da su da yunwa, kuma dole iyalansu su biya kudi dala 10,000, don ceto ransu daga masu safararsu da suka yi garkuwa da su.

Wani matashi ya ce azabtar da shi ne saboda ya gaza biyan dala dubu 8.

“Ka gode wa Allah idan aka saka ka a kurkuku in ba haka ba, wani lokacin wanda ka ke yi wa aiki shi da kansa zai kamaka ya mika wa ‘yan sanda su azabtar da kai, domin kar ya biya ka hakkinka”, a cewar wani dan ci-rani a Libya.

Sannan ya ce kurkukun a cunkushe a gwamatsa mutane dukkaninsu bakaken fata kuma kullum sai an yi wa kowa bulala goma goma sannan a mayar a kulle.

Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta duniya IOM, ta ce Akalla bakin haure 20,000 ke tsare a cikin yanayin kunci da azabtarwa a kasar Libya.

Libya ta kasance mashigin da ke tsallakawa zuwa Turai, wadanda kuma gungun masu safarar dan adam ke tilasta musu samar da kudade, ta hanyar sayar da su domin Ayyukan wahala wasu kuma cin zarafi mafi yawa ta hanayar yi musu fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.