Africa ta Kudu

Majalisar Afrika ta Kudu zata kada kuri'ar sirri kan Zuma

Masu zanga zanga da ke neman shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma ya sauka daga mukaminsa a birnin Durban, a ranar 7 ga watan Afrilun shekara ta 2017.
Masu zanga zanga da ke neman shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma ya sauka daga mukaminsa a birnin Durban, a ranar 7 ga watan Afrilun shekara ta 2017. REUTERS/Rogan Ward

Kotun kolin Afrika ta Kudu, ta ce zauren majalisar kasar, yana da damar kada kuri’ar amincewa ko akasin haka, kan gwamnatin Shugaban kasar Jacob Zuma a Sirrance.

Talla

Yayin da yake sanar da hukuncin kotun kolin Alkalin alkalan kasar, Mogeong Mogoeng, ya ce kundin tsarin mulkin Africa ta Kudu, ya bai wa kakakin majalisar damar shirya hakan, don haka, a duk lokacin da irin wannan bukata ta taso, kakakin ne ke da ikon shirya hanyar da za’a bi wajen kada kuria’ar.

Matakin dai ya karawa Zuma nauyin matsin lambar da yake fuskanta na ya sauka daga mukaminsa daga 'yan adawar kasar.

Jam’iyyun adawa a Africa ta Kudu dai na da kwarin gwiwar cewa, bai wa zauren majalisar damar kada kuri’ar goyon baya ko akasinsa ga gwamnatin Zuma, zai karfafawa ‘yan majalisar da suka fito daga jamiyya mai mullki ta ANC, damar kin goyon bayan Zuma ba tare da fargabar komai, sabanin idan salon zaben ‘yar tinke za’a yi, wato ido na ganin ido.

Shugaban Afrika ta Kudu dai ya dade yana fuskantar matsin lambar ya sauka daga mukaminsa, sakamakon zarge-zargen da suka hada da cin hanci da rashawa, da kuma garambawul din da yayi wa majalisar ministocinsa, inda ya kori ministan kudin kasar Pravin Gordhan.

A baya, kakakin majalisar Afrika ta Kudun, Baleka Mbete, daya daga cikin jiga jigan jam’iyya mai mulki ta ANC, ya musanta cewa, dokar kasar ta haramtawa majalisar kada kuri’ar aminta ko rashinta ga shugabancin Zuma a sirrance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.