Bissau Guinea

Gwamnatin Guinea Bissau ta dakatar da wasu kaffafen yada labarai na Portugal

kasar Guinee Bissau
kasar Guinee Bissau

A Guinea Bisseau hukumomin wannan kasa sun dau mataki na dakatar da wasu kaffafen yada labarai na kasar Portugal dake yadda shirye –shiryen su zuwa wannan kasa ,sanarwa daga Ministan sadarwa na Guinea Bissau Victor Pereira.

Talla

Dokar da ta shafi gidan talabijen na kasar Portugal RTP da wani gidan rediyo na gwamnatin kasar ta Portugal dake yada shirye-shiryen su zuwa Guinea Bissau mai suna RDP bayan da aka same su da laifi keta dokokin ayyukan jarida kamar dai yada ya ke rubucce a sharadin da bangarorin da suka hada da gwamnatin Portugal da Guinea Bissau suka sakawa hannu.

Hukumomin Bissau sun jadadda cewa mudin gwamnatin Portugal ta ki amince a sake komawa teburin tattaunawa domin sake duba yarjejeniya to babu batun sake baiwa wadanan kaffafen yada labarai damar watsa shirye-shiryen su zuwa kasar ta Bissau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.