Najeriya

An kawo karshen cutar sankarau a Najeriya

Hukumomin a Najeriya sun bayyana cewa an kawo karshen cutar sankarau da akayi fama da ita a wasu jihohin kasar.Cutar da ta hadasa mutuwar mutane 1.166 cikin jihohi 25 na kasar. 

Yaki da cutar Sankarau a Najeriya
Yaki da cutar Sankarau a Najeriya africa-online.com
Talla

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai a Abuja, inda Ministan ya bayyana cewa cikin jihohi 25 kusan mutane 14.518 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da ita cutar, sakamakon bicncike na baya-baya nan dake tabbatar da cewa suna ci gaba da sa ido zuwa wadanan yankuna, na nuna cewa ana samu sakamako mai kyau dangane da yaki da cutar .

A shekara ta 2015 mutane 13.700 ne suka kamu da cutar ta sankarau kuma wasu 1.100 ne suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI