Cote d’Ivoire

Kotu ta dage sauraren karar Michel Gbagbo

Laurent Gbagbo Tsohon Shugaban kasar Cote D'Ivoire
Laurent Gbagbo Tsohon Shugaban kasar Cote D'Ivoire ICC-CPI

A Cote D’Ivoire lauya mai kare Michel Gbagbo dan tsohon Shugaban kasar ya sanar da manema labarai cewa kotun kasar ta sake dake zaman sauraren karar da ake yiwa Michel Gbagbo zuwa ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2017.

Talla

Ana zargin dan tsohon Shugaban kasar ta Cote D’Ivoire Michel Bagbo da wani na kusa gare shi Laurent Despas da yada labarai da kan iya harzuka jama’a ga bore.

Michel Gbagbo a wata zantawa da wata jarida mai zaman kan ta ya bayyana cewa Gwamnatin kasar ta na ci gaba da tsare mutane 250 ,yayinda wasu 300 da ake tuhuma suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.