Kamaru

'Yan Mata 4 Sun Kai Harin Kunar Bakin Wake A Kamaru

Wasu mata 4 ‘yar kunar bakin wake sun tasar da bama-bamai da ke jikinsu a garin Mora da ke arewacin kasar Kamaru, yankin da ke fama da hare-hare daga  ‘yan kungiyar Boko Haram.

Sojan karo-karo dake kasar Kamaru a lokacin da suke sintiri domin farautar 'yan ta'addan Boko Haram.
Sojan karo-karo dake kasar Kamaru a lokacin da suke sintiri domin farautar 'yan ta'addan Boko Haram. AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Shaidu sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, matan sun tarwatsa kansu, inda kuma suka kashe wasu fararen hula da dama a wannan gari da ke dab da kan iyakar kasar ta Kamaru da Najeriya.

A garin Mora ake da cibiyar Sojan karo-karo na kasashe dake yakar ta'addanci kuma nan ne Sojan Kamaru ke da tarin makamai na yaki.

Majiyoyi na cewa 'yan matan na shirin kutsa kai cikin gari ne a lokacin da kungiyoyin sa kai suka gansu inda nan take 'yan matan suka tasar da bama-bamai da suka yi jigida da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI