Africa

Sahel: Macron ya kaddamar da rundunar dakarun kasashen G5

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana fatan ganin rundunar hadin gwiwa ta musamman, ta kasashen G5 na yankin Sahel ta fara aikinta na yakar kungiyoyi masu da’awar jihadi nan da makwanni kadan.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita a barnin Bamako
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita a barnin Bamako REUTERS/Luc Gnago
Talla

Macron ya bayyana haka ne, bayan kammala taron da yayi da shugabannin kasashen Chadi, Burkina Faso, Mali, Nijar da kuma Mauritania, yau Lahadi a birnin Bamako, inda ya kaddamar da rundunar.

A wani labarin kuma mayaka masu da’awar jihadi a kasar Mali, da ke biyayya ga kungiyar Al-Qa’eda, sun yada wani hoton bidiyo da ke nuna wasu mutane 6 da suke garkuwa da su.

Wani da ke bayani cikin harshen turanci a bidiyon, ya nuna mutanen da suka fito daga kasashen Faransa, Colombia, Australia, Romania, Switzerland da kuma Afrika ta Kudu.

Fitar da hoton bidiyon da mayakan al’Qaedan suka yi, ya zo a dai dai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke halartar taron kasashen G5 na yankin Sahel a Mali, da suka hada da, Chadi, Muritania, Nijar, Burkina Faso, kan lalubo bakin zaren murkushe ‘yan ta’adda a yankin, inda kuma ya kaddamar da fara aikin rundunar hadin gwiwar kasashen mai kunshe da sojoji 5,000.

Har yanzu ma’aikatar harkokin wajen Faransa ba ta ce komai ba, dangane da sabon bidiyon, sai dai takwararta ta Romania, ta tabbatar da cewa, mayakan sun sace dan kasar, Lulian Ghergut a wurin hakar ma’adanai na Burkina Faso, a watan Afrilun shekara ta 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI