Bakonmu a Yau

Alhaji Aliyu Ikira Bilbis, kan Biafra

Sauti 03:36
Tutar neman kasar Biafra
Tutar neman kasar Biafra STEFAN HEUNIS / AFP

Shugabannin al’ummar Igbo a fagen siyasar Najeriya sun ce ba sa goyon bayan ballewar yankin kudu maso gabashin kasar domin kafa kasar Biafra, inda suka ce a maimakon haka, suna fata a sake fasalta tsarin siyasa wanda Niajeriya ke tafiyar akansa a yau. Domin jin tasirin wannan matsayi da manyan ‘yan siyasar yankin suka dauka bayan sun gana da mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon ministan yada labaran Najeriya Aliyu Ikira Bilbis.