Najeriya

Dan Masanin Kano Maitama Sule ya rasu

Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule
Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule RFI Hausa

Allah Ya yi wa Dakta Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano rasuwa a yau Litinin bayan ya dade yana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce ya rasu ne a kasar Masar bayan an tafi da shi domin diba lafiyarsa.

Talla

Alhaji Maitama Sule ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin Kano ta fitar, ta ce da misalin karfe 4 na yamma bayan Sallar La'asar za a yi Jana'izarsa a fadar Sarkin Kano.

Sannan Gwamnatin Kano ta ware gobe Talata a matsayin ranar hutu domin jimamin rasuwar Dan Masani.

Dan Masanin Kano fitacce ne a Najeriya a siyasance da kuma diflomasiya. Ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a Jam’iyyar Alhaji Shehu Shagari ta NPN.

Sannan ya taba rike mukamin Minista da jekadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI