Rundunar sahel na bukatar miliyan 423 na yuro
Wallafawa ranar:
Taron shugabannin kasashe biyar, na yankin Sahel da aka gudanar jiya lahadi a birnin Bamako na kasar Mali, ya ce ana bukatar Euro milyan 423 domin daukar dawainiyar rundunar da za ta yaki ayyukan ta’addanci a cikin kasashen yankin.
A karshen taron, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen biyar da kuma takwaransu na Fransa Emmanuel Macron, Faransa ta fito fili karara ta ce ba za ta iya daukar nauyin rundunar ita kadai ba.
Kasashen biyar, Mali da Nijar da Burkina Faso da Mauritania da kuma Chadi sun amince su bayar da gudunmuwar yuro milyan 10 domin kaddamar da rundunar, bayan da kungiyar Turai ta sanar da nata tallafi na Euro milyan 50.
Shugaban Fransa Emmanuel Macron ya ce yana fatan rundunar ta fara aikin gadan-gadan kafin lokacin bazara mai zuwa, kuma a cewarsa wannan ba aiki ne mai sauki ba, domin runduna ce da za ta kasance a fagen daga, musamman a yankunan iyakokin kasashen da ke fama da barazana.
Za ta yi aiki ne a daidai lokacin da sauran rundunoni da suka hada da Barkhan da kuma MINUSMA ke gudanar da nasu ayyuka a Mali
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya ce fada da ta’addanci alhaki ne da ya rataya a wuyan kasashen duniya ba wai yankin Sahel kawai ba.
Shugaba Keita ya ce ya kamata a fahimci cewa Sahel wani zango ne ga ‘yan ta’adda, amma babbar manufarsu ita ce su tsallaka zuwa sauran kasashe ciki har da na Turai. Saboda haka ya zama wajibi a kara kokari domin samar da kudaden tafiyar da rundunat ta G-5 Sahel domin nasarar murkushe ‘yan ta’addar.
A cikin watan jiya ne Majalisar Dinkin Duniya ta amince kasashen su kafa rundunar da za ta kunshi dakaru dubi biyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu