Shugabannin Tarayyar Afrika na taro a Addis Ababa
Wallafawa ranar:
Kungiyar Tarayyar Afirka za ta fara taronta na tsakiyar shekara a hedikwatarta da ke birnin Addis Ababa na Habasha, taron da shugabannin nahiyar da dama ke halarta.
Taron na wannan karo zai mayar da hankali ne a game da batutuwa da dama da suka hada da rikice-rikice da yadda kungiyar za ta samar wa kanta kudaden da za ta dauki dawainiyar kanta, da kuma yadda za a bai wa matasan nahiyar dama ta fannin saka-jari da kafa masana’antu a nahiyar.
Sannan shugabannin za su tattauna sabbin shawarwari kan yadda za a yi wa wasu daga cikin dokokin tafiyar da kungiyar ta Afirka garambawul domin su dace da tafiyar zamani da kuma manyan kalubalen da ke gaban nahiyar.
Sai dai za a gudanar da taron ne ba tare da Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari ba, shugabannin manyan kasashen Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu