Cote d'Ivoire

Bangaren fitar da man Feutr a Cote d'Ivoire ya shiga wani hali saboda yajin aiki

Abidjan na kasar Cote d'Ivoire
Abidjan na kasar Cote d'Ivoire

Ma’aikatan kamfanin man fetur din kasar Cote d’Ivoire (Pétroci) sun tsunduma cikin yajin aikin nuna bacin rai a game da abinda suka kira tabarbarewar ayyukan tafiyar da kamfanin mallakar gwamnatin kasar, kamar yadda kungiyar kwadagon ta sanar a Abidjan.

Talla

Bayan kiran da kungiyar kwadagon ta (SYNTEPCI) ta yi, a yau talata ma’aikatan sun tsundumma cikin yajin aiki marar wa’adi, har sai in sun samu biyan bukata, na dakatar da kashe kashen kudi marar misiltuwa da suka ce daraktan kamfanin na yi, a tafiye tafiye da yake yi a jiragen haya shi ka dai, da kuma bada kwangiloli marasa ma’ana domin ci gaba da karkata kudaden kamfanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI