Sojin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan Al-Shabaab
Wallafawa ranar:
Kasar Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare kan mayakan Al-Shabab a kasar Somalia, shi ne karo na biyu cikin wannan wata an Yuli.
Mai magana da yawun sojin Amurka dake kula da nahiyar Africa Patrik Barnes, ya ce nan gaba kadan zasu bayyana irin nasarorin da suka samu a harin da suka kai wa mayakan Al-Shabaab.
A cewar Barnes, burin Amurka shi ne taimakawa Somalia domin murkushe ‘yan kungiyar Al-Shabab don kasar ta sami kwanciyar hankali.
Tun a shekara ta 2007 Al-Shabaab da ke alaka da Al-Qa’eda ke fafutukar ganin ta hambarar da gwamnatin Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu