Bakonmu a Yau

‘Yakubu Dogara’ Najeriya na cikin dokar ta baci

Sauti 03:37
Yakubu Dogara Kakakin Majalisar wakilan Najeriya
Yakubu Dogara Kakakin Majalisar wakilan Najeriya

Kakakin Majalisar wakilan Najeriya  Najeriya, Yakubu Dogara, ya ce kasar na cikin dokar ta baci idan aka yi la’akari da yawan dakarun Sojin da aka baza a jihohin kasar 28 domin bada tsaro.Mista Yakubu da ke ankarar da al’ummar kasar, ya ce abin damuwa ne a ce Sojoji sun karbe ayyukan da ya kamata a ce ‘yan sanda ko jami’an fararen hula na gudanarwa a fanni bai wa kasa tsaro, alhalin Najeriya kasa ce ta Demokrudiya.Akan wannan batu, Umaymah Sani Abdulmumin, ta tuntunbi Dakta Jibril Ibrahim, da ke tsokaci kan al’amuran yau da kullum a Najeriya, Ga kuma yadda hirarsu ta kaya.