Bakonmu a Yau

Majalisar dattawa ta bukaci Yemi Osinbajo ya gaggauta tube Ibrahim Magu

Sauti 03:43
shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu
shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo da ya gaggauta tube Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar yaki da rashawa ta kasar EFCC, sannan suka bukaci ya janye wata sanarwa da ya fitar a baya, da ke cewa ba dole ba ne a nemi amincewar majalisar kafin nada wasu mukamai.

Talla

Sau biyu a can baya majalisar na watsi da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar ta EFCC, to amma duk da haka a lokacin shugaba Muhammadu Buhari ya ci gaba da barin sa kan mukaminsa.

Dr Kailani Muhammad, jigo ne a jam’iyyar APC da ke mulki a Najeriya, ga abinda yake cewa dangane da wannan barazana da ‘yan majalisar suka furta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.