Ghana

Mutane 17 ne suka mutu a wani ramin hako zinari na kasar Ghana

Aikin hako zinari a Afrika
Aikin hako zinari a Afrika RFI/David Baché

A kasar Ghana mutane 17 ne wani ramin hako zinari ya rufta da su a wani ma’adini da ake kira Prestea-Nsuta mai tazarar kilomita 300 a yammacin birnin Accra.

Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a yankin mai suna Atsu Dzinaku, ya ce har zuwa daren jiya an ci gaba da aikin ceto a wani rami mai tsawo sama da mita 80 a karkashin kasa, don gano masu sauran numfashi.

Gwamnatin kasar ta Ghana da jimawa ta sha yi kira zuwa mutane dake gudanar da irin wadanan ayyuka ba bisa ka'ida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.