Najeriya

Mutane da dama ne suka mutu a fadan kabilu a Najeriya

A Najeriya akalla mutane 150 ne suka mutu bayan share tsawon yini uku ana fada tsakanin kabilu biyu a jihar Cross River, kamar dai yadda kamfanin dillancin kasar ya ruwaito.

Yan kato da Gora a Najeriya
Yan kato da Gora a Najeriya
Talla

Shugaban hukumar agajin gaggawa a jihar John Inaku, ya bayyana cewa an yi fadan ne a ranar 27 zuwa 29 ga watan jiya tsakanin Wanikade da kuma Wanihem a yankin Yala, sakamakon wata takaddama da ta samo asali daga mallakar filaye, kuma sama da mutane dubu 14 ne suka gudu daga gidajensu a wannan fada mai kama da yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI