Masu gabatar da kara a Faransa sun bukaci kotun da ke shari’ar mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodorin Obiang a birnin Paris ta yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da biyan tarar kudi miliyan 30 na euro kan tuhumarsa da yin facaka da kudaden jama’a. Obiang dai ya musanta zargin, a Shari’ar da ake ba gaban idonsa ba. Awwal Janyau ya tattauna da Sani Rufa’I masanin siyasar Afrika, a Jamhuriyyar Nijar.