Kenya

Tawagar yan kallo ta soma isa kasar Kenya

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta na cikin wadanda za su fafata a zaben shugabancin kasar a cikin watan Agusta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta na cikin wadanda za su fafata a zaben shugabancin kasar a cikin watan Agusta REUTERS/Thomas Mukoya

Tawagar ‘yan kallo a zaben shugabancin kasar Kenya ta isa birnin Nairobi domin fara aiki da sauran jami’an da kuma jam’iyyun siyasar kasar dangane da wannan zabe da za a yi ranar 8 ga watan agusta mai zuwa.

Talla

Ayarin farko na ‘yan kallon ya kunshi mutane 30, yayin da ake sa ran wani ayarin mai kunshe da mutane 32 zai isa a cikin kwanaki kadan masu zuwa a cewar Marietje Schaake shugabar tawagar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.