Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Hatsarin Mota ya kashe mutane 78 a Afirka ta Tsakiya

Akalla mutane 78 suka rasa rayukansu a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sakamakon hadarin da babbar motar da suke ciki ta yi, da ke makare da fasinjoji da kuma kayayyaki.

Hatsarin Mota ya kashe mutane 78 a Afrika ta Tsakiya
Hatsarin Mota ya kashe mutane 78 a Afrika ta Tsakiya AFP PHOTO/MIGUEL MEDINA
Talla

Hadarin da ya jikkata fasinjoji da dama, ya auku ne a garin Bambari, kilo-mita 300 daga babban birnin kasar, Jamhuriyar Afrikan, wato Bangui.

Mafi yawancin fasinjojin da hadarin ya ritsa da su ‘yan kasuwa ne da ke kan hanyar su ta safara, zuwa wata kasuwa da ke cikin garin na Bambari.

Ko da yake har yanzu jami’ai basu kai ga tantance ainahin abin da ya haddasa hadarin ba, wani shaidar gani da ido yace sharara gudu fiye da kima da direban babbar motar ke yi ne ya jawo wannan mummunan hadari.

Ana fargabar yawan wadanda suka rasa rayukansu ya karu, idan aka yi la’akari da yawan wadanda suka jikkata, kwance rai a hannun mai duka, a asibitin garin na Bambari.

Mutane da dama a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, ciki har da ‘yan kasuwa sun saba yin doguwar tafiya cikin manyan motoci makare da fasinjoji fiye da kima, da kuma tarin kayayyaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI