Kotu ta bukaci a wallafa sunayen barayin Najeriya
Wallafawa ranar:
Wata babbar kotun Tarayyar da ke zamanta a Lagos ta umarci gwamnatin kasar ta gaggauta sanar da ‘yan Najeriya sunayen manyan jami’an gwamnati da aka gano sun wawushe dukiyar kasar da kuma yawan adadin kadarorin da aka karbo.
Hukunci da mai shari’a Justice Hadiza Rabiu Shagari ta bayar, ya biyo bayan koken da kungiyar SERAP da ke fafutukar tabbatar da dai-daiton tattalin arziki da shugabanci a Najeriya ta shigar a gabanta.
Gwamnatin Najeriya ta ce akwai sharuddan da ya kamata a cika kafin ta bayyana sunayen mutanen da suka sace dukiyar kasar domin kowa ya san su.
A watan yunin shekarar bara ne gwamnatin Najeriya ta fitar da wasu alkalumma na milyoyin daloli da ta ce ta kwato daga hannun wasu ‘yan siyasa, sai dai har yanzu ba ta bayyana sunayensu ba,
Babbar kotun Tarayyar da ke birnin Lagos ta bukaci gwamnati ta bayyana wa ‘yan kasar sunayen wadanda suka yi ruf da ciki akan dukiyar jama’a.
Awwal Musa Rafsanjani, na kungiyar yaki da rashawa, ya ce wannan shi ne abin da suka jima suna jira, inda ya ce ya kamata gwamnati ta dauki mataki domin bayyana sunayen barayin domin zama darasi ga ‘Yan kasa.
"Bayyana sunayen barayin zai kasance babbar nasara ga yaki da rashawa a Najeriya", a cewar Rafsanjani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu