Najeriya

Sojin Najeriya sun gabatar da ‘yan Boko Haram da suka mika wuya

Jerin 'Yan Boko Haram da suka mika wuya ga Sojin Najeriya
Jerin 'Yan Boko Haram da suka mika wuya ga Sojin Najeriya RFIHAUSA/Bilyaminu

Rundunar sojan Najeriya ta gabatar wa manema labarai da wasu ‘yan kungiyar Boko Haram 57 daga cikin 70 da suka mika kansu ga sojojin kasar, a garin Maiduguri da ke jihar Borno mai fada da matsalar tsaro.

Talla

Rundunar sojin ta tabbatar da cewa wannan adadi, na Daga cikin wasu ‘yan Boko Haram kusan 700 da yanzu haka ke shirin ajiye makamansu domin rungumar zaman lafiya.

Wakilin RFI Hausa a Maiduguri Bilyamin Yusuf na daga cikin ‘yan jaridun da aka gabatar wa mayakan na Boko Haram, kuma ya aiko da rahoto.

Sojin Najeriya sun gabatar wa manema labarai da ‘yan Boko Haram da suka mika wuya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.