Nijar

‘Yan bindiga sun kashe Sojojin Nijar 5 a Midal

Sojojin Nijar da ke fada da 'yan ta'addar Boko Haram na Najeriya
Sojojin Nijar da ke fada da 'yan ta'addar Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar 5 a garin Midal da ke gaf da kan iyakar kasar da Mali. Rahotanni sun ce an kai harin ne a ranar Laraba.

Talla

Garin Midal, a yankin Tassara cikin jihar Tahoua ba ya da nisa da Tazalit, wani gari da ‘yan ta’addar kasar Mali suka tsallako tare da kashe sojoji 22 a cikin watan Oktoban bara.

Jaridar Air-Info ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun shafe kusan sa’o’i uku suna musayar wuta da sojoji bayan sun kaddamar da harin da sanyin safiyar Laraba har sai da jirgin yakin Faransa ya kawo dauki, maharan suka gudu.

Harin na zuwa a yayin da dakarun Nijar ke kokarin ceto mutane kimanin 37 da mayakan Boko Haram suka sace a kauyen Ngalewa kusa da Kabalewa cikin Jihar Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.