Zimbabwe

Zimbabwe: Mugabe ya kashe kudi fiye da kasafin kasarsa kan tafiye-tafiye

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yayin halartar wani taro a birnin Durban.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yayin halartar wani taro a birnin Durban. REUTERS/Rogan Ward

Jaridun Zimbabwe sun rawaito cewa shugaban kasar, Robert Mugabe ya isa kasar Singapore, domin duba lafiyarsa a karo na uku cikin wannan shekara.

Talla

Duk da koma bayan lafiyarsa, Mugabe mai shekaru 93, wanda ya kai ziyara zuwa kasashen waje har sau 10 cikin wannan shekara, ya bayyana niyarsa ta sake neman wa’adin shugabancin kasar na Karin shekaru 5 a zaben da za’a yi a shekara mai zuwa.

Kwanakin baya ne dai mukarraban gwamnatinsa, suka musanta cewa, Mugabe na bingirewa barci a duk lokacin da ya halarci taro saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, a cewarsu yana saukar da idanunsa ne domin hutar da su.

Alkalumman da jami’an gwamnatin kasar suka fitar, sun nuna cewa, Mugabe ya kashe dala miliyan 53 kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a shekarar 2016, ninki biyu kadan jimillar kasafin kudin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.