Bakonmu a Yau

Alhaji Tanko Yakasai kan barazanar raba Najeriya

Sauti 03:33
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra http://naijagists.com

Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya sun ce suna sake nazarin umurnin da suka ba ‘Yan Kabilar Igbo na ficewa daga Yankin nan da ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa. Daya daga cikin Dattawan kasar, Alhaji Tanko Yakasai ya ce lalle gazawar Gwamnatin kasar na daukar matakan da suka dace ya haifar da wannan matsala.