Najeriya

Boko Haram ta kashe ‘Yan kato da gora 680 a shekaru uku

'Yan kato da Gora da dama ne suka ji rauni a fada da Boko Haram
'Yan kato da Gora da dama ne suka ji rauni a fada da Boko Haram REUTERS/Akintunde Akinleye

Kungiyar matasan da ke taimakawa sojojin Najeriya wajen yaki da Boko Haram da ake kira Civilian JTF ko kuma kato da gora, tace akalla mambobinta 680 aka kashe a cikin shekaru 3 da suka gabata a Jihar Borno.

Talla

Mai ba kungiyar shawara kan harkokin shari’a Jubril Gunda wanda ya bayyana wadanda aka kashe a matsayin gwarzaye ya ce sun mutu ne sakamakon hare hare daban daban da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a sassan jihar Borno.

Gunda wanda ya yabawa Gwamnatin Jihar Barno da ke tallafa wa ‘Yan kato da gora wajen gudanar da ayyukansu, ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta tallafawa iyalan wadanda aka kashe domin samun sanyi a rayuwarsu.

A 2014 ne matasan suka shiga yaki da Boko Haram tare da samun goyon baya daga rundunar sojin Najeriya da kuma samun tallafi daga gwamnatin Jihar Borno.

Boko Haram ta salwantar da rayukan dubun dubatar mutane tare da raba miliyoya da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.