Da wahala a yi zaben Jamhuriyyar Congo a bana
Wallafawa ranar:
Shugabar Hukumar zaben Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Corneille Nangaa’a ta ce yana da matukar wuya kasar ta gudanar da zaben shugaban kasa a wannan shekara, matakin da ake ganin zai sabawa yarjejeniyar da bangarorin siyasar suka taka.
Jami’ar ta shaidawa manema labarai cewar a halin da suke ciki yanzu haka babu yadda za su iya gudanar da zaben a watan Disamba mai zuwa.
A karkashin yarjejeniyar da bangarorin siyasar kasar suka amince da ita bara, yarjejeniyar ta haramtawa shugaba Joseph Kabila sake takara.
Shugaban ‘yan adawar kasar, Felix Tshikesedi ya ce za su mayar da martanin da ya dace nan gaba kadan.
Shugaban hukumar zaben ta bayar dalilai na tsaro musamman rikici a yankin Kasai da za su sa a dage lokacin zaben da aka amince kafin Disemba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu