Libya

Libya: Ana gwabza fada a gabashin Tripoli

Libya na fama da tashin hankali saboda rashin tsayayyar gwamnati
Libya na fama da tashin hankali saboda rashin tsayayyar gwamnati AFP/Abdullah Doma

An samu barkewar kazamin fada a gabashin Tripoli tsakanin dakarun da ke biyayya ga gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnatin ‘yan adawa a Garabulli.

Talla

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne tsakanin dakarun da ke biyayya ga tsohon Firaminista Khalifa Ghweil wanda ya ki amincewa da gwamnatin hadin kai da ke samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Libya ta fito ta yi watsi da farmakin wanda ta kira hari akan Tripoli.

An hambarar da Ghweil ne daga madafan ikon Libya bayan kafa gwamnatin hadin kai a watan Maris na 2016.

Fafatwar ta dada fito da rashin goyan bayan da Gwamnatin hadin kan ke samu daga wasu bangarori.

Kasar Libya na ci gaba da zama dandalin tashin hankali sakamakon rashin Gwamnati mai karfi.

Libya ta fada cikin rikici tun kawar da gwamnatin Marigayi Kanal Ghaddafi a 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.