Africa

Africa:Magungunan jabu sun yi sanadin mutuwar yara dubu 122

Hukumomin Kasashen Afirka ta Yamma sun sake bayyana aniyar su ta dakile yaduwar magunguna marasa inganci da ake sayarwa marasa lafiya a yankin.

Wasu daga cikin magungunan jabu da aka kame a nahiyar Afrika
Wasu daga cikin magungunan jabu da aka kame a nahiyar Afrika http://brazzanews.fr
Talla

Masana sun yi ittifakin cewa magungunan na Jabu, basa taimakawa wajen magance cututuka, sai ma kara cutarwa da kuma haddasa hasarar rayukan jama’a.

A taron da suka yi a kasar Liberia, shugabannin kasashe 15 na kungiyar ECOWAS, sun bukaci gudanar da bincike kan masu safarar irin wadannan magunguna da kuma kasashen da ake sarrafa su.

Wata cibiyar binciken cututuka ta Amurka tace a shekarar 2015, yara ‘yan kasa da shekaru 5, dubu 122 suka rasa rayukansu a nahiyar Afirka, saboda shan irin magunguna marasa inganci.

Wata kungiyar dake yaki da magunguna marasa inganci dake da Cibiya a Paris tace magunguna marasa inganci da ake sarrafa su a kasashen China da India, sun mamaye kasuwannin Afirka ta Yamma, kuma sau tari ba’a iya banbanta su da magunguna na ainahi.

A gegfe guda, hukumar kwastam ta duniya, ta sanar da kwace irin wadannan magunguna marasa inganci da suka kai miliyan 113 a tashoshin jiragen ruwa 16 na nahiyar Afirka, kuma 5,000 daga cikin su magunguna ne marasa inganci na mutane da dabbobi.

Wannan ya sa wasu kamfanoni a shekarar 2009 suka bullo da wata dabara na sanya lambar waya a jikin maganin da suke sarrafawa, wanda ke baiwa mutane damar aikewa da sakon kar ta kwana domin tabbatar da sahihancin magungunan.

Bincike ya nuna cewar a shekaru 6 da suka gabata, mutane sama da miliyan 50 suka yi amfani da irin wannan dabara wajen tabbatar da sahihancin magungunan da suke saye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI