Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo

Amurka tayi barazanar sanya takunkumi zuwa hukumomin DR Congo

Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo
Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo REUTERS/Kenny Katombe

Amurka tayi barazanar sanyawa Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo takunkumi muddin kasar taki gudanar da zaben shugaban kasa a karshen wannan shekara kamar yadda aka tsara.

Talla

Mataimakin Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Michele Sison ya ce ba zasu ci gaba da zuba ido suna ganin hukumomin kasar na wasa da hankalin jama’a wajen kin gudanar da zaben kamar yadda aka tsara ba.

Kasar ta Amurka ta kuma bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta huknta daukacin wadanda suke da hannu wajen kin gudanar da zaben.

Suma kasashen Faransa da Birtaniya sun yi gargadi dangane da dage zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.