Cote D'Ivoire

Gwamnatin Cote D'Ivoire na tsare da wasu shugabanin yan Tawaye

Dakarun kasar Cote D'Ivoire
Dakarun kasar Cote D'Ivoire ledernierpoint

Hukumomin kasar Cote d’Ivoire sun bada umurnin tsare shugabanin yan tawayen kasar dake bore domin ganin an biya su kudaden alawus.An tisa keyar shugaban yan tawayen Amadou Ouattara da kakakin sa Megbe Diomande zuwa gidan yarin garin Bouake inda ake tuhumar su da laifin tada hankalin jama’a da kuma gudanar da zanga zanga ba tare da izini ba.

Talla

An dai kama su ne ranar lahadi bayan da yan Sanda suka tarwatsa tawagar su da ta tare hanya saboda abinda suka kira kin biyan su dala 31,000 a matsayin alawus.

Mataimakin shugaban yan Tawayen Aboudou Diakate da ya gudu, ya bayyana fatar ganin an sako su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI