Kasuwanci

Kaucewa biyan haraji babbar matsala ce a Najeriya

Sauti 10:08
Kasuwar cinikin wayoyin salula a Lagos Najeriya
Kasuwar cinikin wayoyin salula a Lagos Najeriya PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Shirin “Kasuwa A Kai Maki Dole” ya diba batun haraji ne a Najeriya musamman yanzu da gwamnatin kasar hankalinta ya koma ga inganta hanyoyin samun kudadeen shiga maimakon dogaro da arzikin fetir, lura da cewa haraji na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi wajen samun kudaden shiga domin biyan bukatun ‘yan kasa.

Talla

Sai dai kuma, Kaucewa biyan haraji, babbar matsala ce a Najeriya, inda akan haka ne a wani mataki na fadakarwa da tilastawa 'yan kasa sauke wannan nauyin, gwamnatin Tarayya ta kebe ranar Alhamis din kowanne mako, domin jawo hankalin al'umma kan muhimmin haraji ga tattalin arzikin kasa.

Shin ko wadanne dalilai ke sa 'yan Najeriya ke kaucewa biyan haraji; shin Talauci ne, ko Jahilci koko Rashin kishin kasa ne? Batutuwan da shirin ya mayar da hankali ke nan akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.