Najeriya

Mutane 19 sun mutu a wani harin kunar bakin wake a Borno

Garin Molai Kallari a Borno
Garin Molai Kallari a Borno

Yan kunar bakin wake hudu ne suka kai harin ta'adanci a Molai Kallari da Molai Sabon Gari.Mutane 19 ne suka mutu,yayinda aka garzaya da mutane 23 asibiti. 

Talla

Kwamishinan yan Sandar jihar Borno Damian Chuku wanda ya tabatar da aukuwar wannan kazamin aiki daga yan ta'ada ya sheidawa manema labarai cewa 12 daga cikin mutanen da suka mutu yan kato da gora.

.Kungiyar matasan da ke taimakawa sojojin Najeriya wajen yaki da Boko Haram da ake kira Civilian JTF ko kuma kato da gora, tace akalla mambobinta 680 aka kashe a cikin shekaru 3 da suka gabata a Jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI