Najeriya

Ya zama wajibi a daina karbo rance daga waje

Ma’aikatar kudadden Najeriya ta ce ya zama tilas kasar ta daina karbo rancen kudadden ketare domin tallafawa kasafin kudinta, inda ta bukaci a mayar da hankali wajen bijiro da hanyoyin samar da kudadde a cikin gida.

Ministan kudin Najeriya Kemi Adeosun
Ministan kudin Najeriya Kemi Adeosun
Talla

Ma’aikatar kudadden Najeriya ta ce ya zama tilas kasar ta daina karbo rancen kudadden ketare domin tallafawa kasafin kudinta, inda ta bukaci a mayar da hankali wajen bijiro da hanyoyin samar da kudadde a cikin gida.

Minsitan kudin kasar, Kemi Adeosun, ta ce ci gaba da ranto kudadde daga ketare na haifar da gibi ga tattalin arziki, musamman a wannan lokacin da kasar ke farfadowa daga komadar tattalin arziki.

 watan fabrairu shekarar bana dai ne Gwamnatin Najeriya ta ce yanzu haka bashin da ake bin ta ya kai sama da Naira tiriliyan 17 wanda ya kunshi har da na jihohi daga sassa daban daban. Shugaban hukumar da ke kula da basusukan gwamnati, Abraham Nwankwo ne ya bayyana kididigar a gaban kwamitin Majalisar Dattawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI