UNICEF

Rabin ‘yan gudun hijirar Afrika yara ne- UNICEF

'Yan Ci-rani na ratsa teku daga Libya domin tsallakawa zuwa Italiya
'Yan Ci-rani na ratsa teku daga Libya domin tsallakawa zuwa Italiya Reuters/Stefano Rellandini

Hukumar Kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta ce yara sama da miliyan 7 ne aka raba da muhallinsu a rikice rikicen da ake samu da kuma yunwa da sauyin yanayi a kasashen da ke Yammaci da Tsakiyar Afrika.

Talla

Rahotan na UNICEF ya ce duk da wannan adadi na yara sama da miliyan bakwai da rikici ya raba da muhalllinsu, akasarinsu sun samu mafaka ne a wasu kasashen Afirka, yayin da daya daga cikin biyar suka yi kokarin tsallakawa nahiyar Turai domin samun rayuwa mai inganci.

Rahotan ya ce mutane sama da rabin miliyan ne suka tsallaka tekun Baharum daga Libya zuwa Italiya a cikin shekaru hudu da suka gabata daga kasashen da ke kudu da sahara ta hanyar bai wa dillalai kudade don yi safarar su ta hanyoyi masu hadari.

UINCEF tace akalla baki 20,000 yanzu haka ke tsare a Libya, kasar da ta kasance babbar hanyar da ake amfani da ita wajen tsallakawa Turai ta teku, kamar yadda alkaluman hukumar kula da safarar baki suka nuna.

Wani dan kasar Gambia mai shekaru 16, Malik, ya ce an kama shi ne lokacin da ya kama hanyar zuwa ci rani domin taimakawa mahaifiyarsa.

Rahotan ya ce matsalar tattalin arziki da yake-yake da kuma sauyin yanayi sun tilastawa mutane miliyan 12 kaura daga Yammaci da Tsakiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI