Mali

Sojojin Faransa sun kashe ‘yan ta’adda da dama a Mali

Rundunar Sojin Barkhane ta Faransa da ke aiki da dakarun Mali domin yakar 'yan ta'adda
Rundunar Sojin Barkhane ta Faransa da ke aiki da dakarun Mali domin yakar 'yan ta'adda RFI/David Baché

Rundunar sojin Faransa ta Barkhane da kuma dakarun Mali sun kashe ‘yan ta’adda da dama bayan kaddamar da farmaki a yankin Gao arewacin kasar. Wannan na zuwa bayan harin da 'yan ta'adda suka kai wa dakarun Mali a yankin.

Talla

Rahotanni sun ce an yi musayar wuta bayan ‘Yan ta’addan sun bude wa jiragen rundunar Barkhane wuta guda biyu masu saukar Angulu a lokacin da suke shawagi, kafin daga bisani dakarun da ke cikin jirgin suka fatattakin mayakan.

Rundunar Barkhane ta ce dakarunta hudu da ke cikin jiragen masu saukar angulu guda biyu sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata motocinsu.

Wannan na zuwa bayan harin kwantar bauna da wasu ‘yan bindiga suka kai wa sojojin Mali a Menaka a ranar Lahadi inda rahotanni suka ce an kashe mutane hudu sannan kimanin 5 daga cikin sojojin suka bata.

‘Yan bindigar kuma sun tafi da motocin sojojin a harin da aka ce ya faru tsakanin Menaka da Gao.

‘Yan tawaye sun kwace ikon Anefis

Rahotanni daga Mali sun ce wasu ‘Yan Tawayen Abzinawa sun kwace wani gari da ke arewacin kasar bayan an kwashe kwanaki suna fafatwa da sojojin gwamnati.

Ahmoudane Ag Ikmasse, wani dan majalisa da ke kusa da Kidal, ya ce tun ranar Talata mayakan Abzinawan suka karbe ikon garin Anefis.

Arewacin Mali ya zama sansanin ‘Yan Tawayen da ke dauke da makamai, wadanda ke kai hari lokaci zuwa lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.