Kamaru

Boko Haram ta kashe mutane 17 a arewacin Kamaru

Mayakan Boko Haram sun sha kai hare haren kunar bakin wake a arewacin Kamaru
Mayakan Boko Haram sun sha kai hare haren kunar bakin wake a arewacin Kamaru AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Hukumomin tsaron Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane 17 a Yankin Arewacin kasar sakamakon wani harin kunar bakin wake da Boko Haram ta kai wanda ya jikkata akalla mutane 45.

Talla

An kai munanan hare hare ne a kasuwar garin Waza dake kusa da iyakar Najeriya lokacin da jama’a ke cikin hada-hadar kasuwanci.

Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier ta ce mutane 17 suka mutu, cikin su har da mutane biyu da suka kai harin, yayin da wasu 45 suka samu munanan raunuka.

Wata mjiya tace an killace garin ba shiga ba fita dan ci gaba da gudanar da bincike domin tantance mutanen da ke ciki.

Yankin Arewacin Kamaru da ke iyaka da Najeriya ya yi fama da hare haren kungiyar Boko Haram da dama.

A watan da ya gabata, mutane 6 aka kashe a wani harin kunar bakin waken da aka kai a Kolofata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.