Najeriya

Najeriya za ta binciki kisan ‘Yan Bakassi a Kamaru

Najeriya ta kira jekadanta Amb. Abbas Salahedine domin bayani kan kisan  'yan kasar a Bakassi a Kamaru
Najeriya ta kira jekadanta Amb. Abbas Salahedine domin bayani kan kisan 'yan kasar a Bakassi a Kamaru dailypost.ng

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudirin gudanar da bincike kan zargin kisan gillar da jami’an tsaron Kamaru suka yi wa ‘Yan kasar 97 a Yankin Bakassi da aka ba Kamaru iko.

Talla

Dan Majalisar Babatunde Kolawole ya gabatar da kudirin inda ya ke bayanin cewar an hallaka mutanen ne saboda sun kasa biyan naira 100,000 a matsayin kudin izinin kamun kifi a Yankin.

Kolawole ya ce wannan mataki ya sabawa yarjejeniyar da aka kulla na kare lafiyar mazauna Yankin.

Akasarin ‘Yan Majalisun sun amince da kudirin na gudanar da binciken.

A ranar 14 ga watan Agusta na shekarar 2008 ne Najeriya ta amince Yankin Bakassi ya koma Mallakin Kamaru domin kawo karshen takaddama da kasashen biyu ke yi tsawon shekaru 15.

Yankin na Bakassi yana kan iyakokin kasashen Biyu ne a yankin kudancinsu, kafin mazauna yankin su kada kuri’ar amincewa su koma karkashin ikon kasar Kamaru a shekarar 1961.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.