Najeriya-Amurka

Amurka zata kame kadarorin yan Najeriya

Amurka ta ce shirye take domin karbe ilahirin kadarorin wasu yan Najeriya da bincike ya gano cewa suna da hannu a batun rashawa.

Diezani Allison-Madueke tsohuwar Ministan man Najeriya
Diezani Allison-Madueke tsohuwar Ministan man Najeriya AFP / Wole Emmanuel
Talla

Sanarwar da kotun Amurka ta sanyawa hannu na bayyana ta yada wasu daga cikin tsofin ministocin Najeriya suka malaki kadarori da suka hada da wani jirgin ruwa na shakatawa na kusan milyan 80 na dalla, zuwa gidaje a Central Park dake New York.

Mataimakin alkalin kotu a Amurka Keneth Blanco ya hakikanta cewa Amurka ba mafakar mahandama.

Sunan tsohuwar ministan man Najeriya na daga cikin mutanen da aka zana.

Tun ayan rantsar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari,wanda a jawabinsa na cika kasar shekaru 55 da yanci kai ya jadada matsayin gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa musamman a bangaren man fetur na kasar.

Buhari wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda zai jagoranci ma'aikatar man Feturi, ya ce gwamnatinsa na samun bayanai akan kudaden da aka sace a ma'aikatar,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI