CAF

CAF za ta tattauna makomar gasar cin kofin Afrika a Morocco

Tambarin hukumar kwallon kafar Afirka CAF
Tambarin hukumar kwallon kafar Afirka CAF

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF na shirin bude babban taronta a Morocco inda ake sa ran tabbatar da sabon tsarin makomar gasar cin kofin Afrika da kuma gasar cin kofin zakarun nahiyar.

Talla

A gobe Talata ne za a soma taron a birnin Rabat na Moroco wanda zai samu halartar shugaban FIFA Gianni Infantino.

Sannan taron zai kunshi masu horar da ‘yan wasa na kasashen Afrika da tsoffin ‘yan wasa wadanda zasu tattauna makomar manyan gasannin nahiyar.

Tsoffin ‘yan wasan da aka gayyata har da Jaya Jay Okocha na Najeriya da Hossam Hassan na Masar da Rabah Madjer na Algeria da Badou Zaki na Morocco.

Tun bayan zabensa, sabon shugaban hukumar kwallon Afrika Ahmad Ahmad ya yi alkawalin sake fasalta tsarin gudanar da kwallon kafa a Afrika.

A taron za a tatattauna dacewar lokacin gudanar da gasar, ko dai a Janairu ko a Fabrairu ko kuma watan Yuni da Yuli.

Watannin Janairu da Fabrairu dai na cin karo da Lig a Turai inda ake jayyaya tsakanin kasashe da Kungiyoyin Turai akan ‘yan wasa domin dawowa su buga wa kasarsu wasa.

Tsohon shugaban CAF Issa Hayatou ya yi watsi da tsarin gudanar da gasar a watan Yuni, inda yak e ganin zafin da ake makawa a lokacin ba zai yi kyau a yi babbar gasa ba musamman a kasashen arewa da yammacin Afrika da kuma matsanancin sanyin da ke a yankin kudancin Afrika a lokacin.

Taron kuma zai tattauna ko za a ci gaba da gasar duk shekaru biyu ko kuma duk bayan shekaru 4 tare da nazari kan yawan tima-timan da zasu buga gasar inda za a diba yiyuwar kara yawan kasashen daga 16 zuwa 24.

Akwai kuma batun kasashen da ya kamata su dauki nauyin gasar inda daga yanzu sai kasar da ke da filayen wasanni 6 maimakon 4 idan har aka kara yawan kasashen da za su haska a gasar.

Shin ko ya kamata a buga gasar duk shekaru hudu? Ko ya kamata a buga gasar a watan Yuni/Yuli maimakon Janairu/Fabarairu? Amsa wadannan tambayoyi na RFI daga 22 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli da za a fitar da sakamako a ranar 18 ga watan Yuli.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.