Kamaru

Sojojin Kamaru 34 sun bata a teku

Yankin Bakassi na Kamaru
Yankin Bakassi na Kamaru AFP / CLEMENT YANGO

Sojoji kamaru kimanin 34 sun bata bayan jirgin ruwan da ke dauke da su ya nutse a teku kudu masu gabashin kasar akan hanyarsu ta zuwa Bakassi a ranar Lahadi.

Talla

Daga cikin sojoji 37 da ke cikin jirgin ruwan an yi nasarar ceto 3 daga cikinsu yayin da har yanzu ake ci gaba da neman 34 da suka bata, kamar yadda ministan tsaron Kamaru Joseph Beti Assomo ya tabbatar.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani akan dalilin faruwar hatsarin jirgin ruwan.

Sojojin da ke cikin jirgin ruwan da suka bata na cikin dakarun Kamaru da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa mai nisa da ke fama da hare haren kungiyar.

Wasu bayanai sun ce tunbatsar teku ne ya haifar da nutsewar jirgin, kuma Shugaban Kamaru Paul Biya ya bayar da umurnin fadada bincike domin gano sojojin da suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.