Nijar

An ceto rayuwar ‘yan ci-rani 23 a hamadar Nijar

Yankin Agadez ya kasance hanyar da ‘Yan Afrika ke bi domin tsallakawa zuwa Libya a nufin shiga kasashen Turai.
Yankin Agadez ya kasance hanyar da ‘Yan Afrika ke bi domin tsallakawa zuwa Libya a nufin shiga kasashen Turai. REUTERS/Akintunde Akinleye

An gano bakin haure 23 ciki har da yaro dan shekaru 7 a Nijar bayan da masu yi masu jagora suka yi watsi da su a cikin dajin hamada da ke arewacin kasar.Wasu daga cikin mutanen da aka gano ‘yan asalin kasar Senegal da kuma Gambia ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Libya daga Agadez.

Talla

Alhaji Lawal Attaher, shugaban kwamitin ceto jama’ar da irin wannan lamari ya rutsa da su a garin Bilma, ya shaidawa RFI Hausa cewa an ceto mutanen ne a wani gari da ake kira Natai bayan masu fataucinsu sun yarda da su a hamada.

Daga cikinsu mutum guda ya mutu, a cewar Alhaji Attaher.

Bayanai sun ce ‘yan ci-ranin sun shafe kwanaki biyu suna tafiya a sararin hamada bayan sun yi kwanaki shida suna jiran direban da ya ajiye su ya gudu.

Yankin Agadez ya kasance hanyar da ‘Yan Afrika ke bi domin tsallakawa zuwa Libya a nufin shiga kasashen Turai.

Daruruwan mutane ne suka mutu a hamada tsakanin Nijar da Libya da nufin tsallakawa zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.