Ghana

Gobara ta tashi a wani sashe na ginin Majalisar dokokin Ghana

gobara ta  tashi a wani sashe na ginin Majalisar
gobara ta tashi a wani sashe na ginin Majalisar REUTERS/Rafael Marchante

Rahotani daga kasar Ghana sun ce an samu gobara a wani sashe na ginin Majalisar dokokin kasar, sai dai wutar ba tayi illa sosai ga ginin ba.Billy Anaglate, mai Magana da yawun ma’aikatar kashe gobarar Ghana, yace an samu gobarar ce a wani daki na buga takardu dake hawa na 10 kuma sun yi nasarar kashe ta ba tare da ta yadu ba.

Talla

Jami’in yace an kaddamar da bincike domin gano abinda ya janyo wannan hatsari.

Hukumomin sun sanar da daukar matakan da suka dace domin gujewa irin wadanan hatsura da kan iya janyo asara mai girma ga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.