Najeriya

Kaddamar da sabon shiri na shirya zabe a PDP

Tutar jama'iyar PDP mai Adawa a Najeriya
Tutar jama'iyar PDP mai Adawa a Najeriya

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta amince ta shirya taron kasa domin karawa kwamitin riko lokacin da zai shirya karbaben zabe bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da shugabancin Ahmed Makarfi.

Talla

Tun bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da shugabancin Ahmed Makarfi a kujerar Shugabancin jam’iyyar ta PDP, shugabanin Jam’iyyar sun gudanar a Abuja da taro da zai basu damar tantance hanyoyin da zasu taimakawa domin dimke baraka a wanna tafiya.

Jam’iyyar ta PDP na kokarin sake dawowa fagen siyasa tun bayan faduwar ta a  zaben Shugaban kasar da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI