Cote D'Ivoire

Kotun ICC zata yanke hunkunci kan Laurent Gbagbo

Zanga-zangar nuna goyan baya zuwa tsohon Shugaban Cote d'ivoire Laurent Gbagbo
Zanga-zangar nuna goyan baya zuwa tsohon Shugaban Cote d'ivoire Laurent Gbagbo Sia KAMBOU / AFP

Yau Kotun hukunta manyan laifufuka dake Hague zata yanke hunkunci kan sakin tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo a ci gaba da shari’ar da ake masa na tada hankalin da yayi sanadiyar hallaka rayuka ko kuma a’a.

Talla

Gbagbo wanda shine tsohon shugaban kasa na farko da aka gurfanar a gaban kotun, ya daukaka kara kan cewar bai dace a ci gaba da tsare shi ba lokacin da ake gudanar da shari’ar.

Tsohon shugaban da kuma shugaban kungiyar yan ina da kisa da ya kafa Charles Ble Goude sun ki amincewa da tuhumar da ake musu na sanadiyar hallaka mutane sama da 3,000 a tashin hankalin da aka samu bayan yaki sauka daga karagar mulki lokacin da ya fadi zabe a shekarar 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.