Nijar

Yaran da ke fadawa rijiya a Maradi sun karu

wani yanki na Maradi a Jamhuriyyar Nijar
wani yanki na Maradi a Jamhuriyyar Nijar AFP

Mahukunta a jihar Maradi a Jamhuriyyar Nijar sun dauki sabbin matakai domin kare rayukan yara kanana, lura da yadda suke fadawa rijiya a lokacin da suke kokarin dibar ruwa. An kiyasta cewa yara 12 ne suka rasa rayukansu a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan a jihar lokacin da suke je rijiya domin janyo ruwa, abin da ya sa mahukuntan suka fitar da gargadi zuwa ga iyaye. Daga Maradi Salissou Issa ya aiko da rahoto.

Talla

Yaran da ke fadawa rijiya a Maradi ya karu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.