Kamaru

Boko Haram: Kamaru na azabtar da mutane

Kungiyar Amnesty Internationale ta ce ana gallazawa daruruwan mutane da ake zargi na da alaka da mayakan Boko Haram a kasar Kamaru.

Amnesty ta ce jami'an tsaro na azabtar da mutane da suke zargi 'yan Boko Haram ne a Kamaru
Amnesty ta ce jami'an tsaro na azabtar da mutane da suke zargi 'yan Boko Haram ne a Kamaru AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Amnesty ta zargi jami’an tsaron da azabtar da mutane akasari a sansanin da sojojin Amurka da Faransa ke aiki.

Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin bil’adama, ta ce ta tantance irin wannan azabtarwar da suka kai 101 wadanda suka shafi kame kan mai uwa da wabi tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017 da aka samu rikicin a kasar.

Rahotan Amnesty ya ce wasu daga cikin wadanda aka azabtar sun mutu. Kuma ta sha rubuta wasika ga hukumomin Kamaru kan wannan batu amma babu amsa.

Amnesty ta kiyasta cewa Boko Haram ta yi sanadin rayuka 1,500 a Kamaru tun kaddamar da yaki a cikin shekarar 2014.

Kakakin ma’aikatan tsaron Kasar ya yi watsi da rahoton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI