Kenya

Cutar kwalera ta barke a kasar Kenya

Kwayoyin cutar Kwalera
Kwayoyin cutar Kwalera DR

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, cutar amey da gudawa ko kwalera ta barke a Kenya,Cutar na matukar barazana ga yankin Afrika da kuma wasu sassa na duniya bayan wasu wakilan kasashen ketare sun kamu da ita a wani babban taro da suka halarta a Nairobi.

Talla

Annobar na ci gaba da yaduwa tun bayan barkewarta a cikin watan Afrilun da ya gabata, in da aka bayana ta a babban birnin Nairobi da kuma manyan sansanonin ‘yan gudun hijira na Dadaada da Kakuma.

Kimanin wakilan kasashe 146 ne suka kamu da Kwalerar bayan wani taro da suka halarta a ranar 22 ga watan yunin da ya gabata a Nairobi, sannan kuma mutane 136 suka sake kamuwa da ita a kasuwar baje koli ta duniya a cikin wanann wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.