Majalisa ta amince da dokar kare masu tsegunta barayin gwamnati
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar da za ta kare mutanen da ke tsegunta wa hukumomi labarin aikata laifufukan da suka shafi cin hanci da rashawa a kasar.
Najeriya ta samar da wannan doka ne domin bai karfafa wa jama’a gwiwa ci gaba da bai wa hukumomin tsaro da kuma na yaki da rashawa irin wadannan labarai da ke bayar da damar gano wadanda ke yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.
Shugaban kwamitin kula da ayyukan shari’a a majalisar dattawan Sanata David Umaru ya ce dokar za ta bai wa jama’a kariya domin sanar da mai unguwa, dagaci, sarakuna, jami’an ‘yan sanda ko kuma ofishin mai shigar da kara na gwamnati idan suna da labaran suka shafi cin hanci ko kuma handema dukiyar gwamnati a sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu